An yi cikakken zama na biyu na taro karo na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11 a ran 8 ga wata, idan aka tantance daftarin dokar hukunta manyan laifuffuka. Wanda aka kara sanya ka'idar girmama da tabbatar da hakkin bil Adam a ciki, hakan ya dace da ka'idar girmama da tabbatar da hakkin bil Adam ta tsarin mulkin kasar.
Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wang Zhaoguo ya bayyana wannan daftari cewa, sabo da tsarin hukunta manyan laifuffuka na tafiya da manyan batutuwan hakkin jama'a ciki har da hakkin 'yanci, an kara sanya ka'idar girmama da tabbatar da hakkin bil Adam cikin dokar hukunta manyan laifuffuka, domin dacewa da tsarin hukunta laifuffuka irin na zaman gurguzu, kuma hukumomin gudanar da shari'a za su bi wannan ka'idar tsarin mulkin kasar yadda ya kamata.(Lami)