Bisa ga tsarin mulkin kasar Sin da sauran dokokin da abin ya shafa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yanzu za ta cika wa'adin aikinta zuwa watan Maris na shekarar 2013 da ke tafe, kafin lokacin kuma, dole ne a zabi sabbin 'yan majalisar.
A yayin da yake bayani a kan daftarin, Mr.Li Jianguo, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma babban sakataren majalisar, ya bayyana cewa, abin lura shi ne, wannan karo na farko ne da za a zabi wakilan jama'ar kasar Sin bai daya a birane da kuma karkara, domin kara nuna daidaito tsakanin jama'a da yankuna da kuma kabilu daban daban.
Bisa ga daftarin, za a kara yawan wakilai ma'aikata da manoma da kuma masu fasahohi, musamman ma wakilai manoma. Baya ga haka, za a kuma kara yawan wakilai mata.(Lubabatu)