in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin samar da guraben aikin yi
2012-03-08 11:20:52 cri

Yayin da ake kokarin bunkasa tattalin arziki a kasar Sin, abu mafi muhimmanci shi ne a kiyaye zaman karko a fannin samun guraben aikin yi, gaskiya ana iya cewa, hakan zai taimaka wajen raya tattalin arziki tare da kiyaye zaman karko na zamantakewar al'umma a kasar.

Dangane da haka, minista Yin Weimin ya nuna cewa,  "Samar da isasshen guraben aikin yi ga jama'ar kasa ita ce babbar matsalar da gwamnatin kasar Sin take fuskantar yayin da take kokarin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar. Yanzu, a takaice, yanayin samar da guraben aikin yi da kasar Sin ke ciki yana da kyau. A shekarar 2011, yawan sabbin guraben aikin yi da aka samar a birane da garuruwa a kasar Sin ya kai miliyan 12 da dubu dari biyu da goma, adadin da ya fi yawa a tarihi. A sa'i daya kuma, a shekarar bara, yawan mutanen da suka gamu da matsalar aikin yi a kasar ya kai kashi 4.1 cikin dari, wato adadin ya kai matsakaicin matsayi in aka kwatanta shi da na da. Ban da wannan kuma, yawan manoman da suka samu guraben aikin yi a birane da garuruwa a shekarar bara ya zarce miliyan goma."

A farkon lokacin da aka tsara shirin raya tattalin arziki bisa shekaru biyar biyar karo na sha biyu a kasar Sin, gwamnatin kasar ta fi mai da hankali kan aikin samar da guraben aikin yi ga jama'ar kasar, hakan ya taimaka sosai yayin da ake gudanar da wannan aiki. A cikin shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta ba da muhimmanci sosai kan aikin samar da guraben aikin yi ga daliban da suka gama karatun jami'o'i, kuma tana kokarin samar da horas a fannin sana'o'i ga manoman da suka kaura zuwa birane da garuruwa domin neman samun aikin yi da wasu mazauna birane da garuruwa da suke fama da matsalar rashin aikin yi.

Duk da haka, a halin yanzu, gwamnatin kasar Sin tana fama da matsalar samar da aikin yi ga jama'ar kasar,. Kan wannan batu, minista Yin Weimin ya nuna cewa, yanzu, akwai matsala da ake fuskantar a fannoni biyu wato mutanen dake bukatar guraben aikin yi sun yi yawa, misali, bana, yawan mutanen dake fama da matsalar rashin aikin yi a birane da garuruwa ya kai miliyan 25, kuma manoman da suka kaura zuwa birane da garuruwa domin samun aikin yi sun kai miliyan 9 zuwa goma, amma, a sa'i daya kuma, mutanen da yawan gaske suna fama da matsalar rashin aikin yi, musamman ma daliban da suka gama karatun jama'o'i ba da dadewa ba, da kyar, sun iya samun aikin yi mai gamsarwa.

Yin Weimin ya jaddada cewa, ko da yake gwamnatin kasar Sin tana fuskantar matsin lamba wajen samar da guraben aikin yi, amma tana kokarin daukar matakai bi da bi domin kyautata zaman rayuwar jama'a. Ya ce,  "Da farko, gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da manufar da ta dace domin kara samar da guraben aikin yi, na biyu, kara karfafa aikin horas da sana'a domin daga matsayin aiki na 'yan kwadago, na uku, taikamawa rukunin mutanen da suka fi bukatar aikin yi, sannan na hudu, sa kaimi ga wasu mutane da su kafa kamfanoni da kansu, na biyar, samar da aikin hidima don taimakawa masu neman aikin yi."

Kan batun matsalar aikin yi, ana iya cewa, matsalar da daliban da suka gama karatun jami'o'i ke fama ta fi tsanani. Ko wace shekara, dalibai da yawa ne suke gama karatu a jami'o'i, amma da wuya su samu aikin yi masu gamsarwa. A dalilin haka, gwamnatin kasar Sin za ta cigaba da mai da hankali kan daidaita wannan batu, game da wannan, Yin Weimin ya ce,  "Da farko, ana kokarin samar da guraben aikin yi da suka dace da daliban da suka gama karatu a jami'o'i, daga baya, ana kokarin sa kaimi gare su domin su je su yi aiki a kananan garuruwa da yankunan dake yammacin kasar ko kafa kamfanoni da kansu, hakan zai kara samar da guraben aikin yi, a karshe, kara karfafa aikin hidima wajen samar da aikin yi gare su."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China