in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikacin haya na kasar Sin Lin Jianhai ya zama sabon babban sakataren asusun IMF
2012-03-08 11:06:31 cri

A ranar 7 ga wata, shugabar asusun bada lamuni na duniya wato IMF Christine Legarde ta sanar da cewa, an nada ma'aikacin asusun daga kasar Sin mai suna Lin Jianhai a matsayin sabon babban sakataren asusun. Zai fara aiki daga ranar 22 ga watan Maris. Lin Jinhai ya zama dan kasar Sin na farko da ya zama wannan muhimmin matsayi.

Legarde ta nuna a cikin sanarwar da ta gabatar a wannan rana da cewa, Lin Jianhai yana da fifiko kan nazarin aiki da manufofin kasashe membobin asusun, sabo da haka zai bada taimako wajen gudanar da aikin asusun.

Ban da wannan kuma, Legarde ta bayyana cewa, majalisar gudanarwa ta asusun tana fuskantar kalubale, Lin Jianhai zai taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga cimma daidaito a tsakanin ma'aikata da shugabanni da kasashe membobin asusun, da kuma gudanar da ayyukan asusun yadda ya kamata.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China