A gun bikin, shugabar gamayyar kungiyar mata ta kasar Sin Madam Chen Zhili ta taya mata na kasashen daban daban murnar wannan rana, kuma ta bayyana ci gaban da harkokin mata ya samu cikin shekarar 2011.
Haka kuma, Madam Chen ta ce, kamata ya yi mata na kasashen duniya su inganta mu'amala da hadin gwiwa, da karfafa zumunci, da nuna wa juna goyon baya, don kara ba da gudummawa wajen tabbatar da dauwamammen zaman lafiya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa, da kafa duniya mai jituwa.(Bako)