Mista Chen ya ce, har kullum kasar Sin ta kan mutunta ka'idojin kungiyoyin kasa da kasa da ta shiga ciki, amma ba ta da hakkin bin dokokin da wasu kasashe suka kafa, wadanda ba su karkashin ka'idojin wadannan kungiyoyin kasa da kasa. Kasar Sin tana fatan yin shawarwari tare da kasashen da suka zarge ta kan batun biyan haraji, don kara samun fahimta tsakanin juna.
Har wa yau kuma, Mista Chen ya ce, har kullum kasar Sin tana mutunta alkawarin da kungiyar kasashen G20 ta dauka, na kaucewa daukar sabbin matakan bada kariya ga harkokin ciniki, da kuma kare ikon kamfanoninta.(Murtala)