in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta aiwatar da manufar da ta dace domin bunkasa tattalin arziki yadda ya kamata
2012-03-07 10:44:37 cri

A karkashin halin tattalin arziki a gida da na waje da ake ciki yanzu, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da manufar bunkasa tattalin arziki sannu a hankali a shekarar bana tare da daidaita hulda tsakanin ayyuka daban daban kamar su karuwar tattalin arziki sannu a hankali, daidaita karuwar farashin kayayyaki, kyautata tsarin tattalin arziki, kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa, cigaba da yin kwaskwarima kan harkokin tattalin arziki da ingiza zaman jituwa yadda ya kamata.

A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar za ta kara mai da hankali kan hulda tsakanin muhimman ayyuka uku wato cigaba da bunkasa tattalin arziki yadda ya kamata, kyautata tsarin tattalin arziki da daidaita matsalar raguwar darajar kudi. Dangane da haka ne, minista Xie Xuren ya bayanin cewa,  "A shekarar bana, gwamnatin kasar Sin za ta aiwatar da manufar tattalin arzikin da ta dace, ba ma kawai za ta aiwatar da manufa mai yakini ba, har ma za ta cigaba da yin kokarin daidaita matsalolin da ake fuskantar wajen tattalin arziki bisa hangen nesa."

Xie Xuren ya cigaba da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta himmatu kan aikin raya tattalin arziki daga fannoni da dama da muka ambata a baya, na farko, kara kyautata manufar rage harajin da ake bugawa, na biyu, kara kudin shiga na mazauna birane da garuruwa, sannan na uku, kara kyautata tsarin harkokin kudi domin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa, na hudu, hanzartar da sauyawar hanyar bunkasuwar tattalin arziki.

Xie Xuren ya ce, bara, harkokin kudi a kasar Sin sun samu karuwa bisa babban mataki, hakan ya samar da sharuda nagari ga aikin ingiza yalwatuwar ayyuka daban daban kamar su kyautata zaman rayuwar jama'a, kyautata tsarin tattalin arziki da sauransu.

Ya ce,  "An samu kudin shiga daga harkokin kudi daga jama'ar kasa, a dalilin haka, ya kamata a yi amfani su kan aikin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar, musamman ma wajen samar da kayayyakin jama'a da hudimar jama'a."

Mun samu labari cewa, bana, ma'aikatar kudi ta kasar Sin za ta kara mai da hankali kan ayyukan da suka shafi tsimin makamashi, kiyaye muhalli da rage yawan fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Ban da wannan kuma, za ta kara zuba jari kan aikin noma domin kara bunkasa aikin yadda ya kamata.

Xie Xuren ya jaddada cewa, bana, gwamnatin kasar Sin za ta kara kyautata tsarin tattalin arziki wato za ta kara zuba jari kan aikin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa, musamman ma a kananan garuruwa, kauyuka, wuraren dake yammacin kasar da kuma shiyyoyin dake fama da talauci. A sa'i daya kuma, za ta kara zuba jari kan ayyukan da suka shafi ba da ilmi, likitanci, kiwon lafiya, tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a, samar da guraben aikin yi, samar da gidajen kwana, bunkasa al'adun jama'a da sauransu.

Game da wannan, Xie Xuren ya ce,  "Tabbatar da tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a da kyautata zaman rayuwar jama'a sun fi muhimmanci yayin da muke kokarin bunkasa tattalin arziki da sha'anin zamantakewar al'umma, su ma ayyuka mafi muhimmanci ne na harkokin kudi na kasar, dole ne mu kara mai da hankali kansu."

Xie Xuren ya nuna cewa, bana, gwamnatin kasar Sin za ta kara himma kan aikin kyautata zaman rayuwar jama'a.

Daga kasafin kudin da aka yi, yawan kudin da za a kashe kan ayyukan da suka shafi zaman rayuwar jama'a kamar su ba da ilmi, kiwon lafiya, samar da guraben aikin yi, samar da gidajen kwana da al'adu zai kai fiye da kudin Sin Renminbi biliyan 1300, wato ya karu da kashi 19.8 cikin dari in aka kwatanta shi da na shekarar da ta gabata, kuma za a cimma burin karuwar kudin da za a kashe kan aikin ba da ilmi zuwa kashi 4 cikin dari dake cikin kwatankwacin yawan kudin da za a samu daga sarrafa dukiyar kasa a bana.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China