in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta nace kan manyan tsare-tsare na bude kofa ga kasashen waje da samun moriyar juna cikin nasara
2012-03-06 22:03:19 cri
A ranar 6 ga wata, a gun taron manema labaru a lokacin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ministan harkokin wajen kasar Sin Mr. Yang Jiechi ya yi bayani game da manufar diplomasiyya ta kasar Sin da dangantakar da ke tsakaninta da kasashen waje.

Mr. Yang ya ce, "Kyautata yanayin da ake ciki a duniya, da neman hadin gwiwa da kasashen waje, da sa kaimi da yin gyare-gyare, da kafa sigar musamman, kana da ba da gudummawa" a takaice su ne harkokin diplomasiyya da Sin ta samu cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, tare da jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samun damar samun bunkasuwa bisa manyan tsare-tsare cikin shekaru 10 masu zuwa, kuma Sin za ta ci gaba da nacewa bin manufar diplomasiyya na zaman lafiya da dogara ga kanta, da tsayawa tsayin daka kan hanyar bunkasuwa cikin lumana, da dagewa kan manyan tsare-tsare na bude kofa ga kasashen waje da samun moriyar juna cikin nasara.

Bisa rahoton aikin gwamnati da firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya bayar a gun taron majalisar wakilan jama'a, an ce, a cikin shekara mai zuwa, za a kara raya harkokin diplomasiyya na Sin don kara ba da hidima wajen aikin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da saka kasar tafiya da zamani, don ba da gudummawa wajen sa kaimi ga samun karuwar tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. A karkashin wannan aiki, minista Yang Jiechi ya kara bayanin kan abubuwan da za su fi muhimmanci cikin aikin diplomasiyya na bana, ya ce,"Abubuwan da za su fi muhimmanci cikin aikin diplomasiyya na bana su ne, kasar Sin za ta canja salon raya tattalin arziki, da magance kalubale da hadarin da take fuskanta daga kasashen waje, don kara kawo yanayi mai kyau wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da tsayawa kan tabbatar da mulkin kai da harkokin tsaro na kasar, don kara sa himma wajen daidaita manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya ta hanyar yin shawarwari, musamman ma game da batutuwan da suka fi daukan hankalin jama'a, kamata ya yi Sin ta sauke nauyin dake bisa wuyanta."

Yanzu, yanayin duniya da ake ciki na samu sarkakkiya, kuma rikicin kudi na duniya na ci gaba da kunno kai, kuma ana samun tafiyar hawainiya wajen raya tattalin arziki na duniya. Haka kuma, an samu matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da tsaron makamashi da tabbatar da samun isasshen abinci. Yang Jiechi ya ce, shekaru masu zuwa za su kasance muhimman shekaru 10 ga kasar Sin wajen raya zaman lafiya da samun bunkasuwa, ya ce, "Shekaru 10 masu zuwa, za su kasance shekaru 10 ne wajen samun sauyin yanayin da ake ciki da gaggauta samun bunkasuwa, kana za su kasance shekaru 10 ne wajen samun damar warware matsaloli a karkashin babban sauyin da aka samu a duniya, kamata ya yi a mai da hankali wajen canja salon raya tattalin arziki, da kokarta shiga cikin hadin gwiwa da kasashen duniya da samun sabon fiffiko wajen yin takara da kasashen waje, a karkashin yanayi na dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya."

Haka kuma, daga bara, an kara mai da hankali sosai game da dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen da ke makwabtaka da ita, Mr Yang Jiechi ya ce,"Kasar Sin ta zama babbar kawa ce wajen harkokin cinikayya ta akasarin kasashen da ke makwabtaka da ita, kuma jimillar cinikayyar da ke tsakaninmu da sauran kasashen Asiya ta zarce dalar Amurka biliyan 1000, kuma mun saka jarin da yawansa ya kai dalar Amurka kimanin biliyan 20, kuma mun zurfafa hadin gwiwa a fannonin kimiyya da fasaha, da hada-hadar kudi, da makamashi, kana da manyan ayyuka da ba a taba ganin irinsu ba, ko da yake, akwai sabanin da ke tsakaninmu da wasu kasashen da ke makwabtaka da mu, amma muna kokarin dukafa ka'in da na'in wajen warware sabani ta hanyar yin shawarwari."

A cikin taron manema labaru da aka dade har na tsawon awoyi 2, Mr. Yang shi ma ya bayyana matsayin da Sin ke tsayawa game da dangantakar da ke tsakain kasashen Sin da Rasha, da Sin da India, da Sin da Japan, da batun zirin Koriya, batun kasar Siriya, da dangantakar da ke tsakaninta da Afrika.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China