Mr.Xie Xuren ya yi wannan furuci ne a yayin da yake halartar taron manema labarai da aka shirya dangane da babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da a halin yanzu ake yi a nan birnin Beijing. Ya ce, a shekarar bana, za a kara ware kudi ta fannonin harkokin ba da ilmi, kuma za a yi kokarin ganin yawan kudin da aka zuba zai kai kashi 4% na GDP na kasar. Sa'an nan, za a gaggauta raya tsarin ba da kariya ga zaman al'umma, da inganta gyare-gyaren tsarin samar da magani da kiwon lafiya. Ban da haka, za a yi kokarin gina gidaje masu rahusa domin talakawa, tare kuma da bunkasa harkokin al'adu. (Lubabatu)