in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba ta lamunta ba da ko wace kasa a yankin gabas ta tsakiya ta mallaki makaman nukiliya
2012-03-06 17:19:02 cri

A safiyar yau 6 ga wata, a nan birnin Beijing, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya ce, game da batun nukiliyar kasar Iran, Sin na kan matsayin kin yarda da ko wace kasa a yankin gabas ta tsakiya da ta mallaki makaman nukiliya , ciki har da kasar Iran. Sa'i daya kuma, a ganin kasar Sin, ko wace kasa na da hakkin yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana kuma bisa wasu ka'idoji.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana game da taro karo na 5 na majalisar wakilai na 11 na jama'ar kasar Sin, Yang Jiechi ya ce, neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya ya dace da moriyar jama'ar kasashen dake wannan yanki, kuma ya dace da moriyar kasashen duniya. Hakan ya sa, ya zama ginshiki da Sin ta dogara a kai wajen magance wasu matsaloli a wannan yanki.

Ya kara da cewa, a ganin kasar Sin, ya kamata, a yi shawarwari maimakon nuna kiyaya ga juna, kuma yin hadin kai maimakon sanya takunkumi. Sin ba ta amince ba da ko wace kasa ta dauki salon sanya takunkumi na kashin kanta. Kasashe da yawa na duniya suna daukar wannan matsayi.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China