in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya yi kira ga gamayyar kasashen duniya da su nuna goyon baya ga aikin shimfida zaman lafiya da neman samun ci gaba a nahiyar Afrika
2012-03-06 16:36:29 cri

A ran 6 ga wata a nan birnin Beijing, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, ya kamata zaman al'ummar kasashen duniya su nuna goyon baya ga aikin shimfida zaman lafiya da neman samun ci gaba a nahiyar Afrika

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana game da taro karo na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 11, Yang Jiechi ya ce, ya kamata gamayyar kasashen duniya su sa himma wajen raya aikin shimfida zaman lafiya da neman samun ci gaba a nahiyar Afrika.Hakan zai nuna goyon baya ga kasashen Afrika da su warware batutuwansu da kansu da kuma neman bunkasuwar su da kansu, ta yadda kasashen za su kara taka muhimmiyar rawar ta a zo a ganin a fannin more hakkinsu cikin harkokin kasa da kasa.

Yang Jiechi ya ce, kasar Sin na da alfarma sosai , sabo da jama'ar kasashen Afrika sun dauke ta a matsayin ainihin babbar abokiyarsu, kuma ta yi niyyar sauke nauyin dake bisa wuyanta. Kasar Sin , kasa ce mai tasowa, tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen Afrika domin raya makomarsu yadda za ta kasance mai kyau.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China