A gun taron manema labaru na taro na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 11 da aka gudanar a wannan rana, Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin da wasu kasashen Larabawa suna da bambancin ra'ayoyi kan wasu batutuwa, amma suna da ra'ayi iri daya wajen kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa a yankin gabas ta tsakiya. Ba za a iya kawo illa ga zumuncin dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa ba.
Game da batun Syria, Yang Jiechi ya ce, ra'ayin kasar Sin, musamman jawabin kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ya jawo hankalin kasa da kasa sosai, kana an kara samun fahimtar juna da goyon baya daga sauran kasashen duniya.(Zainab)