in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin sarrafa karuwar farashin kayayyaki bisa kashi 4 cikin dari a shekarar 2012
2012-03-06 10:55:54 cri

Mazauna birnin Beijing su kan fada cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, farashin kayan lambu, nama, kifi, shinkafa da sauran abinci ya karu sosai, kafin wannan, ko wane wata, mutane uku na kashe kudin Sin Renminbi wajen dubu daya a kansu kawai, amma, yanzu, ana kashe a kalla sama da dubu biyu."

Dangane da haka, mazauna birnin Tianjing sun bayyana cewa, "A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, farashin ruwan famfo ya sake karuwa, hakika, ruwa, lantarki da gas sun fi muhimmanci ga zaman rayuwarmu na yau da kullum, dole ne mu yi amfani da su a ko da yaushe, muna cikin zulumi, saboda kila zai sake karuwa nan gaba."

Daga watan Oktoba zuwa watan Disamba na shekarar bara, babban bankin kasar Sin ya yi bincike kan mazauna birane da garuruwa da suka ajiye kudi a bankin, sakamakon da aka samu daga binciken ya nuna cewa, mazauna birane da garuruwa da yawansu ya kai kashi 68.7 cikin dari suna ganin cewa, yanzu farashin kayayyaki ya karu kwarai. A shekarar 2011, yawan karuwar farashin kayayyakin kasar Sin ya kai kashi 5.4 cikin dari, amma yanzu, ana sa ran cewa, za a daidaita shi zuwa kashi 4 cikin dari a shekarar bana.

A karshen shekarar bara, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da cewa, kasar Sin za ta bunkasa tattalin arzikin kasar sannu a hankali a shekarar 2012, wato za a yi kokarin kiyaye farashin kayayyaki tare da tabbatar da zaman karko a kasar. Game da wannan, wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Li Yilong ya nuna cewa,  "Daidaita karuwar farashin kayayyaki zai taimaka wajen kwantar da hankalin jama'ar kasa, sannan zai taimaka wajen bunkasuwar tattalin arziki. Ko da yake, a halin yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya samu yalwatuwa yadda ya kamata, amma farashin kayayyaki yana karuwa duk wayewar gari, idan darajar kudin ta ragu, zaman rayuwar jama'ar kasa zai gamu da matsala. Shi ya sa, dole ne a kara mai da hankali kan farashin kayayyaki."

A ran 5 ga wata, direktan kwamitin ci gaba da yin kwaskwarima kan tattalin arzikin kasar Sin Zhang Ping ya nuna cewa, yanzu, gwamnatin kasar Sin tana fuskantar wasu kalubalen da suka shafi karuwar farashin kayayyaki, amma, ya hakikance cewa, za a cimma burin daidaita karuwar farashin kayayyaki zuwa kashi 4 cikin dari a shekarar bana. Zhang Ping ya ce,  "Kawo yanzu, mun riga mun samu sakamako masu faranta rai, misali, mun cimma burin cigaba da samun karuwar yawan hatsi har na tsawon shekaru takwas, muna gudanar da harkokin tattalin arziki daga duk fannoni yadda ya kamata, gaskiya, na hakikance cewa, za a cimma burin daidaita karuwar farashin kayayyaki zuwa kashi 4 cikin dari a bana."

A ran nan da safe, a cikin nashi rahoton game da aikin gwamnati, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao shi ma ya jaddada cewa, sarrafa karuwar farashin kayayyaki shi ne ya fi muhimmanci ga moriyar jama'ar kasa tare da cimma burin bunkasa tattalin arziki sannu a hankali. Saboda haka, dole ne gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin sarrafa karuwar farashin kayayyaki. Firayin minista Wen Jiabao ya ce,  "Ya kamata gwamnatin kasar Sin ta cigaba da sarrafa karuwar farashin kayayyaki, musamman ma kan farashin abinci, hakan zai taimaka wajen samar da isasshen kayayyakin lambu ga jama'ar kasa tare da daukar mataki kan matsalolin da abin ya shafa kamarsu bayar da labaran da ba su da tushe, ajiye kayayyaki domin neman kazamar riba, sanya farashi kamar yadda suke so da sauransu. Mun sa ran cewa, masu samar da kayayyaki da masu saye za su samu moriya tare bayan kokarin da muka yi."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China