in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a birnin Beijing
2012-03-05 17:45:14 cri

An bude taro karo na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 11 a ran 5 ga wata da safe a birnin Beijing. Inda shugabannin kasar Sin da wakilai kimanin 3000 na jama'ar kasar Sin suka halarci taron.

Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayar da rahoto kan ayyukan gwamnatin kasar. Inda ya bayyana cewa, wannan shekara ce mafi muhimmanci a shirin shekaru biyar-biyar na 12, kuma ita ce shekarar karshe ta wa'adin gwamnatin kasar Sin ta yanzu, za a yi kokarin samun gamsuwa daga jama'a.

Wen Jiabao ya bayyana cewa, babban burin da aka tsara kan bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin shi ne, yawan karuwar GDP zai kai kashi 7.5 cikin dari, yawan karuwar sabbin guraban ayyukan yi a birane da garuruwa zai kai miliyan 9 ko fiye, kuma yawan mutanen da suka rasa guraban ayyukan yi ba zai kai kashi 4.6 cikin dari ba, kana yawan hauhawar farashin kayayyaki (CPI) ba zai kai kashi 4 cikin dari ba. Albashin da mazaunan birane da garuruwan kasar suke samu zai karu tare da bunkasuwar tattalin arziki gaba daya.

Wen Jiabao ya ce, ya kamata gwamnatin kasar Sin ta mayar da batun kyautata zaman rayuwar jama'a a matsayin aiki mafi muhimmanci. Gwamnati za ta gyara tsarin kudin harkokin zaman al'umma, kana za ta kara ware kudi don inganta zaman rayuwar jama'a da tarbiyya da al'adu da kiwon lafiya da samar da guraban ayyukan yi da ba da tabbaci ga zaman al'umma da kuma gina gidajen jama'a. Bugu da kari, za a gyara tsarin amfani da motocin gwamnati da rage kudin kashewa na hukumomi daban daban na gwamnatin kasar.

Ban da wadannan kuma, Wen Jiabao ya gabatar da muhimmiyar dawainiyar yin gyare-gyare, wato ci gaba da gyara tsarin hada-hadar kudi, bunkasa kamfannoni masu zaman kansu da na gwamnati gaba daya, ci gaba da yin kwaskwarima kan tsarin farashin kayayyaki, ci gaba da gyara tsarin raba kudin shiga, da kuma gaggauta yin kwaskwarima kan hukumomi masu lura da harkokin yau da kullum na zaman al'umma da kuma gwamnatin kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China