in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a harba tauraron Dan Adam na Chang'e mai lamba uku a lokacin da aka tsara a shekarar 2013
2012-03-05 15:06:37 cri

Ranar Lahadi 4 ga wata, mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin kuma masanin kimiyyar sararin samaniya Ye Peijian ya ce, ana gudanar da aikin kera tauraron Dan Adam na Chang'e mai lamba uku yadda ya kamata, za a harbe shi a lokacin da aka tsara a shekarar 2013.

Ye Peijian ya ce, wannan tauraro na da muhimmanci ta fuskoki guda uku. Da farko, ya banbamta da tauraro mai lamba daya da biyu wadanda ba su iya tsayawa a kan duniyar wata ba kamar taurari 100 ko fiye da Sin ta harba a baya ba, kuma akwai wasu tauraro da kumbuna dake iya dawowa kasa ta laima. A maimako, tauraron Chang'e mai lamba uku na da kafofi abin da ya sa ya iya tsayawa a doron duniyar wata. Na biyu, wannan tauraro na dauke da na'urorin nazari daban-daban. Na uku, wannan tauraro na dauke da wata na'ura mai kama da mota, wanda zai iya gudanar da aikinsa har tsawon watanni uku bayan tauraron ya tsaya kan duniyar wata.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China