in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za su duba rahoton aikin gwamnatin kasar
2012-03-05 14:45:10 cri

A safiyar ran 5 ga wata, hukumar tafiyar da harkokin ikon mulkin kasa mafi girma a kasar Sin wato majalisar wakilan jama'ar kasar ta yi taron da aka saba yinsa sau daya a ko wace shekara a birnin Beijing inda wakilai kusan dubu uku suka taru a babban dakin taron jama'a domin tattauna shirin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin.

A yayin taron da aka bude a ran nan da karfe 9 na safe, a madadin majalisar gudanarwar kasar Sin, firayin ministan kasar Wen Jiabao ya karanta rahoton aikin gwamnatin.

Rahoton ya takaita muhimmann ayyukan da gwamnatin kasar Sin ta yi a cikin shekarar da ta gabata, kuma ya yi bayani kan shirin da aka tsara game da aikin da gwamnatin za ta yi bana. Firayin minista Wen Jiabao ya nuna cewa, shekara ta 2012 tana da ma'ana ta musamman, musamman ma ga gwamnatin kasar Sin. Ya ce,  "Shekarar bana tana da muhimmanci saboda ta kasance a tsakiyar lokacin da ake gudanar da shirin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin bisa shekaru biyar biyar a karo na sha biyu, wato tsakanin shekarar 2011 zuwa ta 2015, shekara ta karshe a wa'adin aiki na gwmanati a wannan karo, a dalilin haka, dole ne mu himmantu kan aikinmu domin kara biyan bukatun jama'ar kasa yadda ya kamata."

Rahoton ya gabatar da wasu muhimman ayyukan da suka shafi bunkasuwar tattalin arziki a kasar Sin a shekarar 2012, wato yawan kudin da za a samu daga sarrafa dukiyar kasa a shekarar 2012 zai kai kashi 7.5 cikin dari, kara samar da guraben aikin yi a birane da garuruwa da yawansu zai kai miliyan tara, rage yawan matsalar aikin yi a birane da garuruwa da kashi 4.6 cikin dari, kayyade karuwar farashin kayayyaki bisa kashi 4 cikin dari, kara yawan kudin da za a samu daga shigi da fici zuwa kashi 10 cikin dari tare da kyautata halin da kasar ke ciki wajen ciniki a duniya.

A cikin wadannan ayyukan, aikin da ya shafi yawan kudin da za a samu daga sarrafar dukiyar kasa ya fi jawo hankalin jama'a, saboda shi ne karo na farko da gwamnatin kasar Sin ta nuna cewa, za ta rage yawansa daga kashi 8 cikin dari zuwa kashi 7.5 cikin dari a yanzu, dangane da haka, firayin minista Wen Jiabao ya bayyana cewa,  "Dalilin da ya sa aka tsara shirin rage yawan kudin da za a samu daga sarrafa dukiyar kasa a kasar Sin shi ne domin ana son aiwatar da shirin bunkasa tattalin arziki bisa shekaru biyar biyar karo na sha biyu cikin lumana, nan gaba, za a kara mai da hankali kan aikin sauyin hanyar bunkasa tattalin arziki tare da kyautata ingancin bunkasuwar tattalin arziki, hakan zai taimaka wajen tabbatar da manufar raya tattalin arzikin kasa lami lafiya cikin dogon lokaci."

Amma, idan gwamnatin kasar Sin tana son cimma burin bisa shirin da aka tsara, ana iya cewa, akwai matsala. A cikin nashi rahoton, firayin minista Wen Jiabao ya ce, za a fuskanci matsaloli da kalubale yayin da ake kokarin raya tattalin arziki a kasar Sin. To, ta yaya za a warware wadannan matsaloli? Firayin minista Wen Jiabao ya nuna cewa,  "Yayin da gwamnatin kasar Sin take kokarin kyautata aikinta, abu mafi muhimmanci shi ne dole ne ta daidaita hulda tsakanin ayyuka iri daban daban yadda ya kamata, wadannan muhimman ayyuka sun kunshi samun karuwar tattalin arziki sannu a hankali, sarrafa karuwar farashin kayayyaki, gyara tsarin tattalin arziki, kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa, kara yin gyare-gyaren tattalin arziki tare da ingiza zaman jituwa a kasar."

Ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa, tunanin da aka nuna a cikin wannan rahoton aikin gwamnatin kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta kara mai da hankali kan aikin raya tattalin arziki sannu a hankali a kasar.

A cikin kwanaki tara masu zuwa, wakilai wajen dubu uku dake wakiltar ra'ayi da moriyar jama'ar kasar Sin da yawansu ya kai biliyan daya da miliyan dari uku za su duba wannan rahoton gwamnatin kuma za su jefa kuri'a kansa domin tsara shirin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin na bana.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China