in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da cikakken zama na shekara-shekara na CPPCC
2012-03-03 18:22:48 cri

Yau 3 ga wata da misalin karfe 3 na yamma, an yi bikin kaddamar da cikakken zama na shekara-shekara na CPPCC a nan birnin Beijing, inda shugabannin kasar Sin, kuma mambobin majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, CPPCC kusan 2200 suka halarta, kuma Jia Qinglin, shugaban zaunannen kwamitin majalisar ya bayar da wani jawabi. Game da ayyukan da majalisar ta yi a cikin shekarar da ta gabata, Mr. Jia ya ce, "A cikin shekarar da ta gabata, majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta sauke nauyin dake kanta a tsanake, ciki har da bada shawarwari kan harkokin siyasa, sa ido bisa tafarkin demokuradiyya da sauransu, haka kuma ta nuna himma da kwazo wajen inganta zaman al'umma ta hanyar kimiyya, da shimfida zaman jituwa a tsarin zamantekwar al'umma. Majalisar ta bayar da babbar gudummawa a fannonin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 12, gami da raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi."

Shekara ta 2011, shekara ce da gwamnatin kasar Sin ta soma aiwatar da shirin raya tattalin arziki da kyautata zaman al'umma na shekaru biyar-biyar a karo na 12, inda neman ci gaba ta hanyar kimiyya, da sauya hanyar da ake bi wajen habaka tattalin arziki suka zama batutuwa mafi muhimmanci a cikin shirin. Don haka, bada shawarwari a wannan fanni ya zama wani muhimmin aiki a gaban majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Game da kokarin da membobin majalisar ke yi a wannan fanni, Mista Jia Qinglin ya bayyana cewa, "Membobin majalisar sun nuna hazaka wajen bada kyawawan shawarwari da nasihohi kan wasu muhimman batutuwa na kasar Sin, ciki har da daidaita harkokin kasa daga manyan fannoni, da inganta biyan bukatun cikin gida, da kyautata tsarin masana'antu, da raya ayyukan gona na zamani, da kuma kara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje da sauransu. Wadannan membobi sun gabatar da daftarori sama da dubu 6, da bayar da kyawawan shawarwari da nasihohi da dama, wadanda aka sanya su a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 12 da dai sauran manufofin kasar Sin."

Game da ayyukan da majalisar ba da shawara ta kasar Sin CPPCC za ta yi a shekarar ta 2012, shugaba Jia Qinglin na majalisar ya gabatar da shiri ga taron a fannoni 6. Mr. Jia ya jaddada cewa, kara kokarin bunkasa tattalin arziki da kyau cikin hali mai dorewa da kuma tabbatar da kwanciyar hankali da jituwar zaman al'umma muhimman ayyuka biyu ne da majalisarsa za ta yi a shekarar 2012. Mr. Jia ya ce, "Dole ne a sanya kokarin neman ci gaba bisa ilmin kimiyya a matsayi mafi muhimmanci a lokacin da mambobin majalisar suke sauke nauyinsu. Kuma zaunannen kwamitin majalisar zai yi taron musamman, inda za a yi nazari kan yadda za a kara karfin bunkasa masana'antu domin tabbatar da bunkasa tattalin arziki cikin kyakkyawan hali ba tare da wata tangarda ba. Haka kuma za a tara mambobin jam'iyyun siyasa na dimokuradiyya da na kungiyar masana'antu da 'yan kasuwa da wasu kwamitocin musamman na majalisar da kuma majalisun ba da shawara kan harkokin siyasa na larduna domin neman ra'ayoyinsu kan yadda za a bunkasa tattalin arziki. Bugu da kari, tabbas ne tabbatar da kwanciyar hankali da samar da jituwa a zaman al'ummar kasar Sin ya kasance wani muhimmin nauyi ne da aka dora wa majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin. Sabo da haka, za a shirya tarurukan musamman, inda za a tattauna batun yadda za a kara kula da harkokin zamantakewar kasar a kokarin samar da kyawawan ra'ayoyi da shawarwari ga hukumomin gwamnatin kasar."

Bisa labarin da aka bayar, an ce, ya zuwa tsakar ranar Asabar 2 ga wata, a cikin takardu kusan dari 8 da mambobin majalisar suka gabatarwa cikakken zama na shekara-shekara na majalisar, mambobi da yawa sun ba da ra'ayoyinsu kan yadda za a kara mai da hankali kan bunkasa masana'antu. Madam Cai Ling, mambar majalisar 'yar jam'iyyar kafa kasar ta hanyar dimokuradiyya, ta kuma gabatar da wata takarda, game da wannan takarda, madam Cai ta bayyana cewa, "Game da yadda za a kara mai da hankali kan bunkasa masana'antu, yau ina son gabatar muku wata takardar da jam'iyyarmu ta gabatar wa babban taron. A cikin wannan takarda, mun jaddada cewa, dole ne a bunkasa tattalin arzikin masana'antu domin karfafa tushen tattalin arziki. Jam'iyyarmu wadda ke kunshe da dimbin masu tafiyar da tattalin arziki tana kula da matsakaita da kananan masana'antu da masana'antu masu zaman kansu da dai makamatansu cikin shekaru da yawa da suka gabata. Bisa binciken da muka yi, mun gabatar da wannan takarda ga babban taron majalisar."

Bisa rahoton da Mr. Jia ya bayar game da ayyukan da majalisar CPPCC ta yi a shekarar 2011, da kuma wanda za ta yi a shekarar 2012, lokacin da take kula da tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, za ta kara yin kokarin yada al'adun kasar da kuma kara yin cudanya da hadin gwiwa da kasashen waje domin bayar da gudummawarta wajen sada zumunci tsakanin jama'ar kasar Sin da sauran kasashen duniya. (Sanusi Chen Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China