in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batutuwan kyautata zaman rayuwar jama'a sun kara jawo hankalin jama'a kafin budewar taruka biyu a kasar Sin
2012-03-01 14:47:54 cri

A farkon watan Maris da muke ciki, za a kira taruka biyu wato taro na 5 karo na 11 na babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da taro na 5 karo na 11 na babban taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a Beijing, babban birnin kasar. Kafin budewar tarukan biyu, batutuwan da suka shafi zaman rayuwar jama'ar kasa kamar su kara samun kudin shiga, sarrafa farashin gidajen kwana, tabbatar da adalci kan tsarin ba da ilmi sun kara jawo hankalin jama'ar kasar.

Xiao Yu tana aiki ne a birnin Beijing bayan da ta gama karatun jami'a a shekarar 2009, kuma an haife ta a birnin Tianjing dake kusa da Beijing. A halin yanzu, ba ta nuna gamsuwar zaman rayuwarta a nan Beijing ba, ta ce,  "Na yi shekaru biyu ina aiki a Beijing, na kashe kusan dukkan kudin da na samu daga aikin bada hayar gidan kwana da motar tasi, kudi kadan suka rage. Ina fatan zan iya kara samun kudi nan gaba domin kyautata zaman rayuwata."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, yawan kudin da aka kashe kan zaman rayuwa a manyan biranen kasar Sin ya kara karuwa bisa babban mataki, a dalilin haka, batutuwan da suka shafi zaman rayuwar jama'a kamar su farashin kayayyaki, gidajen kwana, abinci mai tsabta sun fi jawo hankalin jama'ar kasar. Bisa kididdigar da aka yi a karshen watan da ya wuce, an ce, bara, matsakaicin yawan kudin da aka samu daga sarrafar dukiyar kasa na kowanen mutum a biranen Shanghai, Beijing da Hangzhou ya kai sama da Renminbi Yuan dubu tamanin, wato ya kai kusan dalar Amurka dubu 12 ke nan. Bisa ma'aunin bankin duniya a shekarar 2010, ana iya cewa, matsayin kudin shiga na wadannan biranen ya riga ya kai matsayi na kasashe masu arziki, amma hakika, ba haka abin yake ba. Dangane da wannan batu, shehun malamin dake aiki a kwalejin koyon ilmin tattalin arziki dake jami'ar masana'antu da kasuwanci ta Beijing Zhou Qingjie ya nuna cewa, karuwar yawan kudin da aka samu daga sarrafar dukiyar kasa ba zai janyo jin dadin zaman rayuwar jama'ar kasa kai tsaye ba. Ya ce,  "Yawan kudin da aka samu daga sarrafar dukiyar kasa basu zuwa daidai da batun jin dadin zaman rayuwa, saboda ma'anar GDP tana nufin yawan kayayyakin da aka samar a cikin shekara daya, amma ba a lura da matsalolin da jama'ar kasa suke fuskatar a yayin da ake samar da wadannan kayayyaki ba, misali, gurbatar muhalli, samar da kayayyakin da ba su da inganci da abincin da ba su da tsabta, ban da wannan kuma, a kasa kula da rarar kudin shiga tsakanin masu arziki da masu fama da talauci, sai dai, a kasa kula da tsawon lokacin aiki na mutane daban daban, shi ya sa, bai kamata ba a fada cewa, jama'ar kasar suna jin dadin zaman rayuwa sakamakon karuwar GDP."

A dalilin haka, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai kan aiki game da yadda za a kara kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa ta hanyar yin amfani da sakamakon da aka samu. Bara, an zartas da shirin raya tattalin arzikin kasar Sin na shekaru biyar biyar na karo na sha biyu inda gwamnatin kasar Sin ta tsai da cewa, za ta cigaba da kokarin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa tare da bunkasa tattalin arzikin kasar.

Game da wannan, shehun malami Gu Shengzu, wakilin majalisar wakilan duk jama'ar kasar Sin kuma masanin ilmin tattalin arziki ya nuna cewa, hakan ya nuna mana cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin biyan bukatun jama'ar kasa na kara masu jin dadin zaman rayuwa.

Gu Shengzu ya ce,  "Abu mafi muhimmanci a cikin shirin raya tattalin arzikin kasar Sin na shekaru biyar biyar na karo na sha biyu shi ne kara kudin shiga na jama'ar kasa tare da bunkasa tattalin arziki, wato jama'ar kasar suna iya kara samun kudin shiga sakamakon bunkasuwar tattalin arziki."

Gaskiya batutuwan zaman rayuwar jama'a suna da muhimmanci saboda suna da nasaba da zaman jituwar zamantakewar al'ummar kasa. To, ta yaya za a tattauna batutuwan a yayin taruka biyu da za a kira?, bari mu sa ido mu gani.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China