A wannan rana, tawagar gwamnatin tarayyar Nijeriya da ta kunshe mutane 20, ta ziyarci wata masana'antar samar da wutar lantarki da ke nan birnin Beijing. Bayan ziyarar, a yayin da Orubebe ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, aikin raya harkar wutar lantarki ta kasance wani muhimmin aiki da ke kunshe cikin harkokin raya manyan ayyuka a yankin Nijer-Delta, kuma samar da wuta lantarki zai ba da tabbaci wajen aikin raya masana'antu a yankin. Ya ce, yana fatan masana'antun Sin da na kasar Nijeriya za su anfani da hadin gwiwa da ke tsakaninsu, yanzu kwararru na kasar Nijeriya na yin bincike a masana'antun kasar Sin.
Haka kuma, gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda ya ce, yana fatan inganta hadin gwiwa da masana'antun Sin, tare da fatan koyon salon bunkasa sha'anin wutar lantarki irin na kasar Sin, don raya masana'antun da samar da wutar lantarki a cikin dogon lokaci a kasar Nijeriya. Haka kuma a karkashin inuwar raya sha'anin wutar lantarki, don kara sa kaimi wajen raya sha'anin sake-sake a masaka,da kera takalma da yin sukari na kasar.(Bako)