A ranar 24 ga wata, a nan birnin Beijing, minista mai kula da aikin gine-gine na Nijeriya Bashir Yuguda ya bayyana cewa, ya na fatan kara fadada hanyoyin hadin gwiwa ta bangarorin biyu da ke tsakanin kasar Nijeriya da Sin.Zai zurfafa hadin gwiwa tsakanin masana'antu na kasashen biyu don kara kyautata manyan ayyuka na kasar.
A yayin da Ministan Bashir ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, makasudin ziyarar tawagar tarayyar Nijeriya a kasar Sin ,shi ne don tattauna maganr hadin gwiwa tare da masana'antun kasar Sin game da raya hanyoyi 3 da ke arewaci da kudu maso gabashin kasar, ka na da aikin raya hanyoyin da ke hada birane da kauyuka da birnin Abuja, domin kyautata harkokin sufuri na kasar. Ya ce, ya na fatan yin amfani da wannan dama ta hadin gwiwa tsakaninsu wajen gina hanyoyi, da kara fadada wasu sauran gine-gine, wadanda suka hada da aikin gyran wutar lantarki, da aikin gona, da abubuwan more rayuwa ,da harkar sadarwa.
Tuni, shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya sanar da cewa, zai yi iyakacin kokari shi don raya fanin gina hanyoyi na kasar, domin kara raya lamuren tattalin arziki da zamantakewar al'umma na kasar. Daga bisani kuma, Nijeriya ta kara inganta hadin gwiwa da masana'antun kasar Sin wajen gine-ginen hanyoyi, da shinfida layin dogo ,da aikin zirga-zirgar jiragen sama, kuma a gudanar da dukkan ayyuka lami lafiya.(Bako)