in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron majalisar kasashe membobin kungiyar hadin gwiwar musulmai karo na 7 a kasar Indonesia
2012-02-01 14:52:27 cri

A ran 31 ga watan Janairu, aka rufe taron majalisar kasashe membobin na kungiyar musulmai (PUIC) karo na 7. An shafe kwanaki biyu a birnin Palembang na kasar Indonesia ana gudanar da taron, kasashe 40 daga cikin kasashe membobi 51 na kungiyar sun halarci wannan taro. Inda aka tattauna sosai kan wasu muhimman batutuwa, a ciki har da maganar bunkasuwar tattalin arziki.

Shugaban kasar Indonesia Susilo Bambang Yudhonoyo, ya yi jawabi a gun taron da cewa, yawan mutanen kasashen musulmai ya kai kashi 20 cikin dari na daukacin al'ummar duniya, amma yawan kayayyakin da suke sarafawa zuwa kasuwannin duniya, kashi 7 ne kawai cikin dari. Susilo Bambang Yudhonoyo ya jaddada cewa, a halin yanzu da ake fama da rikicin siyasa da na tattalin arziki a duniya, dole ne kasashen musulmai su kara hadin gwiwa domin kara karfinsu na tattalin arziki sabili da su tunkari kalubale da ke a gabansu.

Ban da haka kuma, Susilo Bambang Yudhonoyo ya nuna cewa, a game da wasu batutuwa na kasa da kasa, kasashen musulmai sun rasa ikon bayyana ra'ayinsu, dole ne gwamnatoci da majalisun kasashen musulmai su taka muhimmiyar rawa kan lamuran da ke gudana a duniya. Kungiyar PUIC tana da karfin tabbatar da kudurin hada-hadar kudi ta hadin gwiwar tattalin arziki na kasa da kasa, ta yadda za a kawo karshen rikicin al'adu da ya barke a sakamakon tabarbarewar tattalin arziki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China