Gagarumin shagalin da ya hada kan baki fiye da dari uku, ciki kuwa har da shugabannin kasashe, ministocin harkokin waje da kungiyoyin kasa da kasa, an yi shi ne a wajen majalisar dokoki ta kasa, maimakon a bainar hadin gwiwar 'yan majalisun dattajai da wakilai, wanda hakan ke da nufin samar da isasshen fage ga wadanda aka gayyata wajen bikin.
Wannan ne dai karo na farko, da aka samu sauyin gwamnati cikin ruwan sanyi a dimukradiyyance, tun bayan matsanancin yakin basasar kasar da aka kwashe tsawon shekaru 15 ana yi.
Da take yin jawabin kaddamar da ita, Sirleaf ta bukaci 'yan uwanta 'yan kasar da su hada hannu da sabuwar gwamnati don samar da makoma ta gari, ci gaba da samun hadin kai a kasar.
Sirleaf ta ce, gwamnatin zata mayar da hankali wajen bunkasa bangaren matasa don kirkiro damar samun ayyukan yi da zasu ba da tallafi ta fannin tattalin arziki wajen gina kasa.
Shugabar ta Laberiya ta bayyana cewar, abubuwan da suka abku ciki kuwa har da na boren da ya jawo zub da jini a watan Nuwamba, wanda ya juya hannun agogo baya a kasar, lamura ne dake nuna rashin hakurin matasa. (Garba)