Da farko, Yaya Toure mai shekaru 28 a duniya ya shiga jerin sunayen 'yan wasa a zaben bayan da ya lashe mashahurin dan wasan kasar Cote d'Ivoire Didier Yves Drogba, dan wasan kasar Ghana George Boateng wato Prince na AC Milan, dan wasan kasar Kamaru Samuel Eto'o da kuma dan wasan kasar Cote d'Ivoire Gervais Yao Kouassi. A zaben, Yaya Toure ya lashe Andre Ayew daga kasar Ghana da kuma Seydou Keita inda ya zama dan wasan kwallon kafa mafi kyau a nahiyar Afirka na shekarar 2011.
A halin yanzu, kungiyar Manchester City ce a matsayin farko a gasar Premier ta kasar Ingila, Yaya Toure yana taka muhimmiyar rawa tare da taimakawa kungiyar wajen samun wannan sakamako mai kyau. Wannan ne karo na farko da Yaya Toure ya samu lambar yabo ta dan wasan kwallon kafa mafi kyau na nahiyar Afirka, wadda ita ce lambar yabo ta koli a dandalin wasan kwallon kafa na Afirka. Kana ya zama dan wasan kasar Cote d'Ivoire na biyu da samun wannan lambar yabo bayan da Drogba ya samu wannan lambar yabo.