Shirin gudanar da allurar da zai dauki kwanaki 4, da asusun taimakawa yara na MDD wato UNICEF, da hukumar kiwon lafiya ta MDD, da kuma Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sudan ta Kudu suka dauki nauyin gudanarwa, zai bada damar cimma yara sama da dubu dari uku dake da shekaru kasa da 5. Wanan shi ne zagaye na 4 kuma na karshe a wanan shekara, bayan wanda aka gudanar a cikin watan Feburairu, Maris da kuma Nuwamba, inda yara sama da miliyan 3.2 su ka ci moriyar shirin.
Paulo Okech Ajah, jami'in hukumar kiwon lafiya ta MDD ya furta cewa, suna kokarin yiwa yara 'yan kasa da shekaru 5 rigakafin sama da dubu dari uku a wanan shekara, sun kuma fadada gudanar da yin sallura a yankin jihar Nilo. Ya kara da cewa, a cikin watan Feburairu sun cimma kishi dari bisa dari na yaran da ya kamata a yi musu sallura, kishi dari da daya a cikin watan Maris, a yayin da watan Nuwamba suka samu kishi dari da biyu, kuma a wanan karo suna fatan zarce hakan.
Ana samun cutar shan inna ta wasu kwayoyin cuta da ake dauka. Cutar shan inna na kama kwakwalwa ta kuma nakasar da yaro dukkan tsawon rayuwar shi, yaro daya cikin dari 2 na kasancewa hakan.
A halin yanzu kasashe 4 ne a duniya suka kasance sansanin cutar shan inna, Afghanistan, Indiya, Najeriya da kuma Pakistan duk da yawan masu kamuwa da cutar na raguwa a cikin shekaru 25 da suka gabata.
Cutar shan inna ta bullo ne a kudancin Sudan a cikin watan Afrilu na shekara ta 2008, amma bayan gudanar da allurar rigakafin kamuwa da cutar babu duriyar ta sake bullowa har watan Yuni na shekara ta 2009. An dai kawar da cutar a yankin Nilo, kamar yadda Fazal Ather jami'in hukumar MDD mai kula da kiwon lafiya ya sanar. (Halilou)