Wannan fuskar butun butumin ta kasance daya daga cikin manyan kayayyakin da suka yi suna dake bayyana wani alamar karamin akwatin Kota da ta samo asali daga kudu maso gabashin kasar Gabon da aka saida ita a shagon Christie's dake Londres a cikin watan Yunin da ya gabata, in ji mista Robert Orngo-Berre wani masanin irin wadannan fuskoki.
"Daya daga cikin abun dake banbanta wannan fuskar shi ne kyan gani da siffarta da wasu alamomin na musammun da aka daidaita," kamar yadda masanin ya bayyana a cikin jaridun kasar.
Fuskar na da wuyar samu da kuma tarihinta ya nuna ta zauna hannun fitaccen dan kasuwar kayayyakin zamani da kayayyakin tarihi na barkar fata Charles Ratton kafin ta kima hannun wani masanin kayayyakin sassaka na Afrika Hubert Goldet.
Bayan mutuwarsa an saida wannan fuskar miliyan 200 na Sefa a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2000. Kuma an gabatar da ita cikin fina finai da bajen kolin kayayyakin sassaka.
Sai da wannan fuskar ba ta cimma matsayin koli ba wajen tsada a shekarar 2006 bisa wata fuskar Ngil da ta fito daga yankin Woleu Ntem a arewacin kasar da aka saida miliyan biyar kudin Euro. (Maman Ada)