A ran 17 ga wata da dare, kumbon Shenzhou mai lamba takwas ya isa wani filin da ke tsakiyar yankin Mongoliya ta gida na kasar Sin, ta haka, cibiyar kula da zirga-zirgar sararin samaniya ta birnin Beijing ta inganta wasu sabbin fasahohi masu muhimmanci ta fuskar sarrafa kumbo, kuma kumbon Tiangong mai lamba daya da na Shenzhou mai lamba takwas sun hadu kana sun rabu da juna cikin nasara kamar yadda aka sarrafa su a kasa.