A lokacin zantawar, da farko Nasr ya yi godiya ga kasar Sin saboda girmama zaben da jama'ar kasar Libya suka yi, kana ya nuna yabo sosai ga matsayin da kasar Sin ke tsayawa a kai. Ya kara da cewa, kasar Sin kasa ce dake sada zumunci da kasar Libya, kasashen biyu suna da moriya iri daya, kasar Libya kuma za ta aiwatar da hadin gwiwa a dukkan fannoni tare da Sin.
A ranar 31 ga watan Oktoba ne, kwamitin wucin gadi na kasar Libya ya jefa kuri'a, inda aka zabi Abdel-Rahim al-Keeb a matsayin shugaban kwamitin zartaswa na wucin gadi na kasar. A cikin makonni biyu masu zuwa zai yi shawarwari tare da bangarori daban daban kan batun kafa gwamnatin wucin gadi. Kan maganar ko Al-Keeb zai iya kafa gwamnatin wucin gadi yadda ya kamata cikin lokaci, ko a'a, Nasr ya yi imanin cewa, Al-Keeb na gudanar da hakikanan ayyuka ne ba bisa karfin siyasa ba, kuma yana kokarin kafa gwamnatin da za ta mai da hankali kan ra'ayin jama'a.
Wace irin hanya ce kasar Libya za ta bi wajen aiwatar da harkokin mulki ta yadda za ta kasance batun da ke jawo hankalin bangarori daban daban? A yanayin da ake ciki na sabanin da ke kasancewa game da hanyar da za a zaba na tsarin dimokuradiyya ko tafarkin addinin musulunci a harkokin mulkin kasar Libya, Nasr ya bayyana cewa, kasar Libya za ta zama kasar da za ta iya amincewa da ra'ayoyi daban daban ba tare da yin la'akari da wasu bambance-bambance ba. A karkashin sabon mulkin kasar, za a yi amfani da tsarin addinin Musulunci da kuma dimokuradiyya tare. Nasr yana ganin cewa, addinin Musulunci da dimokuradiyya na iya zama a hurumi guda, har ma za a iya hade su waje guda don samun bunkasuwa tare.
Bayan haka kuma, Nasr ya jaddada cewa, an yi zaben shugaban kwamitin zartaswa na wucin gadi na kasar Libya ne bisa tsarin dimokuradiyya, kuma cikin adalci. Ya kara da cewa, ko shakka babu kasar Libya kasa ce mai bin tsarin addinin Musulunci, saboda babu wasu addinai a kasar ban da addinin Musulunci. Amma, kasar Libya kuma za ta zama kasar da ke bin tsarin dimokuradiyya mai bude kofa ga kasashen waje.
A yayin da yake magana game da yunkurin sake raya kasar Libya, Nasr ya ce, Al-Keeb ya riga ya gabatar da shirin ayyukan da za a aiwatar a cikin watanni 8, inda aka mai da hankali kan sake gina biranen da aka rushe sakamakon rikicin da aka fuskanta a kasar, da kuma sake farfado da zaman karko na kasar. Ban da wannan kuma, akwai wasu abubuwan dake kunshe cikin shirin share fage kan zaben wakilan kasar, da sauransu.
Nasr ya kara da cewa, kwamitin wucin gadi na kasar Libya na kokarin zaben wakilai a cikin watanni 8, don kammala ayyukansa yadda ya kamata. Ya kuma jaddada cewa, mambobin kwamitin wucin gadi ba su bukatar ci gaba da rike ragamar mulkin kasar, domin idan mun yi haka, jama'ar kasar Libya za su hambarar da mu kamar yadda suka yi wa Gaddafi. (Bilkisu)