Liu Zhenming ya ce, batun kasar Afghanistan a cikin wannan lokaci yana da muhimanci, kuma samara da kasar Afghanistan da zai kasance cikin zaman lafiya da zaman karko da samun 'yancin kai da bunkasuwa ita ce buri daya ga jama'ar kasar da kasashen da ke yankin gamayyar kasa da kasa.
Liu Zhenming ya yi kira ga al'ummomin duniya da su nuna goyon baya ga kasar Afghanistan don ta tabbatar da kokarinta na samun zaman lafiya da tsaro da ingiza aikin samun sulhu ta hanyar dimokuradiya da kuma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar .Sannan ya ce, yayin da kasar Afghanistan ta tabbatar da samun zaman lafiya da bunkasuwa, gwamnatin kasar Sin za ta nuna goyon baya ga jama'ar kasar Afghanistan a kowane lokaci.
A lokacin taron, an zartas da tsarin da aka yi a Istanbul game da yin hadin kai wajen tsaron yankunan Afgannistan , kuma ya jadadda amfanin daidaituwa da MDD ta bayar kan batun kasar Afghanistan, kuma an yi kira ga kasa da kasa da su girmama mallakar kan kasar da cikakken kasar a yayin da suka ba da tallafi ga kasar (Zainab Zhu)