Abdulrahim Rahimah ya kara da cewa, bayan da aka gabatar da sanarwar, galibin wakilan kwamitin wucin gadi na kasar Libya za su isa birnin Tripoli. Bisa labarin da shugaban kwamitin gudanarwar kwamitin wucin gadi na kasar Libya Mahmou Jibril ya bayar, an ce, gwamnatin da ke kan mulkin kasar za ta yi shawarwari kan batun kafa sabuwar gwamnatin wucin gadi bayan da aka gabatar da sanarwar.
A wannan rana, hukumar ICPO ta bayar da wata sanarwa, inda aka bayyana cewa, bayan kungiyar da kotun ICC sun tabbatar da labarin mutuwar Gaddafi, sun yi kira ga Seif al-Islam Qaddafi da ya mika kansa.(Abubakar)