A sa'i daya kuma, wani jami'in kungiyar tsaro ta NATO ya ce, kungiyar NATO ba ta da hakkin tabbatar da da wannan labari, kuma kwamitin NTC ne ke da alhakin sanar da irin wannan labari.
Haka kuma, bisa labarin da kwamandan da muka ambata ya bayar, an ce, an kame Gaddafi a garinsa da ke birnin Sirte, kuma yayin da aka kame shi, an same shi da rauni mai tsanani a kafafuwansa, inda aka kai shi zuwa wani kebabben wuri ta jirgin sama mai saukar ungulu.
Da ma, dakarun NTC sun bayyana cewa, sun kusan mamaye birnin Sirte, kuma yanzu, suna kokarin kakkame ragowar sojoji magoya bayan shugaba Gaddafi.(Bako)