in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"An kame tsohon shugaban kasar Libya Gaddafi", in ji hafsan sojojin kwamitin NTC
2011-10-20 20:33:12 cri

A ranar 20 ga wata, Wani babban kwamandan dakarun kwamintin mulkin wucin gadi ta Libya NTC ya fada wa manema labaru cewa, sun kame tsohon shugaban Libya Kanar Muammar Gaddafi, sai dai har yanzu hukumar Libya ba ta tabbatar da wannan labari ba.

Bisa labarin da wannan kwamandan ya bayar, an ce, an kame Gaddafi a garinsa da ke birnin Sirte, kuma yayin da aka kame shi, an same shi da rauni mai tsanani a kafarsa, kuma yanzu, an kai shi zuwa wani kebabben wuri ta jirgin sama mai saukar ungulu.

Kana, a wannan rana, gidan talebijin din Libya ya bayar da labarin kame Gaddafi, amma hukumar Libya ba ta tabbatar da wannan labari ba.Tukuna da ma, dakarun NTC sun bayyana cewa, sun kusan mamaye birnin Sirte, kuma yanzu, suna kokarin kakkame ragowar sojojin magoya bayan shugaba Gaddafi.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China