Mai magana da yawun rundunar mayakan ta NTC mai lura da kudancin Bani Walid Mahmoud Tawfiq ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua cewa, za su ci gaba da sa ido a kan wannan ayari, sannan za su sanar da takwarorinsu dake yankin da wannan tawaga ta nufa domin daukar mataki.
A game da halin da ake ciki a Bani Walid kuwa dake da tazarar 180km kudu maso gabashin birnin Tripoli, Tawfiq ya bayyana cewa, dakarun kwamitin na NTC suna ci gaba da sintiri a sassa daban daban na birnin kuma sun samu nasarar kame a kalla sojoji 300 masu goyon bayan Gaddafi tare da makamansu.(BAGWAI)