in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ICPO ta soma farautar dan Gaddafi na uku
2011-09-29 21:49:32 cri
A ranar 29 ga wata, kungiyar 'yan sanda ta kasa da kasa ICPO da hedkwatarta ke Lyon na kasar Faransa ta bayar da umurnin cafke dan Gaddafi na uku, Saadi da ke kasar Nijer.

Kungiyar ICPO ta bayar da sanarwa a wannan rana cewa, wannan ne karo na farko da ta bayar da irin wannan sanarwa don biyan bukatun mahukuntan Libya, wato kwamitin wucin gadi na kasar sakamakon tuhumarsa da ake da taba satar kadarori daga kungiyar kula da harkokin kwallon kafan kasar a yayin da yake shugabantar kungiyar.

Bayan haka kuma, kungiyar ta ce, Saadi Gaddafi mai shekaru 38 a duniya yana Nijer a halin yanzu, sakamakon haka, za a nemi taimako daga kasashen Libya da Nijer da su hana shi ziyartar shiyyoyi daban daban a duniya domin cafke da kuma dawo da shi kasar Libya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China