in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Libya sun gano 'yaran Gaddafi biyu
2011-09-29 16:20:40 cri

Ranar Laraba 28 ga wata a birnin Tripoli, kakakin sojojin mahukuntan Libya Omar Bani ya ce, yanzu haka, an gano 'yaran Gaddafi biyu wato Seif Al-Islam da Mutassim, amma har yanzu ba a san inda Gaddafi yake ba.

A gun wani taron manema labaru da aka yi a birnin Tripoli, Omar Bani ya ce, yanzu, sojojin sun sami ci gaba mai kyau cikin yakin da ake yi a birnin Sirte, kuma za su cimma nasara ba da dadewa ba.

Omar Bani ya ce, yanzu, mahukunta ba su mayar da hankali kan inda Gaddafi yake boye ba, aikin da aka sa gaba shi ne 'yantar da dukkan yankunan Libya tare da tabbatar da zaman lafiyar biranen da suka 'yantar. Daga baya, shine za su yi kokarin cafke Gaddafi. A Ko wane yankin iyakar kasa da Gaddafi ya ke boye, mahukunta za su kama shi.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China