in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Libya sun dakatar da kai hari birnin Sirte
2011-09-28 15:05:37 cri

Ranar Talata 27 ga wata, kwamitin wucin gadi na kasar Libya ya dakatar da kai harin a birnin Sirte garin Gaddafi tare da ba ma mazauna garin fararen hula na birnin lokacin tsira da rayukan su. Kwamitin ya kuma baiwa sojojin Gaddafi da suka rage wata dama don mika wuya. A wannan rana kuma, ta gidan rediyo, Gaddafi ya yi jawabi cewa, zai ci gaba da mulkin sa.

Jagoran dakarun kwamitin masu hari kan Sirte ya ce, sojojin mahukunta sun yi musayar ra'ayi tare da tsohon shugaban kabila na birnin Sirte, kuma sun cimma matsaya daya kan dakatar da bude wuta tsakaninsu.

Bisa labarin da gidan telibijin na Al Jazeera ya bayar, an ce, a wannan rana, ta gidan rediyon Bani Walid, Gaddafi ya yi jawabi cewa, yana kasar Libya kuma zai ci gaba da yin dagiya har zuwa karshe .

Kakakin wakilin NATO mai kula da matakin soja da NATO ta dauka kan Libya ya ce, yanzu, kwamitin ya mamaye makamai da makamashin nukiliya dake tsakiya da kudancin kasar. Amma, wasu wurare ciki har da Sirte, Bani Walid da sauransu wadanda suke ci gaba da goyon bayan tsohon gwamnatin suna karkashin mallakar Gaddafi.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China