in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Libya sun cimma nasarar shiga birnin Sirte
2011-09-27 16:10:01 cri

Ran 26 ga wata, dakarun kwamitin wucin gadi na kasar Libya sun cimma nasarar yakin shiga birnin Sirte, sun shiga birni ne daga gabas, amma sauran sojojin Gaddafi ba su daina mayar da martani gare su ba, bangarorin biyu suna ci gaba da yin musayar wuta

A wannan rana kuma, jiragen saman yaki na kungiyar NATO sun sake kai sabbin hare-hare ga birnin Sirte, domin ba da taimako ga kwamitin wucin gadi. Ban da haka kuma, kungiyar NATO ta shaida cewa, jiragen saman yakin nata sun riga sun kai farmaki ga wani dakin ajiye makamai da sauran wuraren ayyukan soja 7 dake kewayen birnin Sirte a ran 25 ga wata.

A sa'i daya kuma, bangarori daban daban suna ci gaba da mayar da hankali kan wurin da Gaddafi da iyalinsa suke boye. Kafofin watsa labaru na kasar Algeria sun bayar da labari a ran 26 ga wata cewa, membobi 8 na iyalin Gaddafi sun riga bar birnin Algeris, babban birnin kasar Algeria zuwa birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar. Amma kasar Masar ta musunta hakan.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China