in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kasar Libya ta yanzu ta gamu da martanin da aka yi musu a birnin Sirte
2011-09-26 14:17:55 cri

A ran 24 ga wata, dakarun kwamitin wucin gadi na kasar Libya sun cimma nasarar shiga birnin Sirte, garin Gaddafi, amma sun gamu da martani sosai da magoya bayan Gaddafi suka yi musu.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru suka bayar, an ce, dakarun kwamitin wucin gadi sun kai farmaki ga birnin daga kudu da gabas a ran 24 ga wata. Wani jami'in kwamitin wucin gadi ya ce, sojoji 7 sun mutu a yayin da sojoji fiye da 140 suka ji rauni bisa sakamakon musayar wuta da aka yi. A ran 24 ga wata da dare, sojojin kwamitin wucin gadi sun janye daga birnin Sirte domin shirya sake kai farmaki ga birnin. Kana a birnin Bani Walid, wani birni na daban ne dake karkashin magoya bayan Gaddafi, dakarun kwamitin wucin gadi suna ci gaba da yin musayar wuta tare da sojojin Gaddafi a wurin waje da birnin.

Kakakin bangaren soja na kwamitin wucin gadi Ahmed Omar Bani ya furta a ran 25 ga wata cewa, garin Ghadames dake a kudu maso yammacin birnin Tripoli ya samu farmaki mai tsanani daga sojojin Gaddafi a ran 24 ga wata da dare. Yanzu, mazauna garin Ghadames sun nemi kwamitin wucin gadi da ya tabbatar da tsaron su.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China