in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dinkin duniya tana taimakawa Libya domin sake ginuwar kasa bayan yaki
2011-09-19 14:30:45 cri

A ranar 16 ga wata, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya zartas da wani kuduri mai lambar 2009 inda aka tsai da cewa, majalisar dinkin duniya za ta aika wa kasar Libya wata kungiyar ta musamman domin samar da taimako ga kasar, wa'adin aikin kungiyar shi ne watanni uku. Wannan ya alamanta cewa, kasar Libya ta fara aikin sake ginuwar kasa bayan yaki a hukunce, wato daga yaki na da. Amma, masu lura da al'amuran yau da kullum sun yi nuni da cewa, a halin yanzu, kasar Libya tana cikin mawuyacin hali, shi ya sa, kila ne za a gamu da wahalhalu masu tsanani yayin da ake gudanar aikin sake ginuwa a kasar.

Bisa labarin da 'yan diplomasiyan da abin ya shafa suka fayyace, an ce, kungiyar musamman da majalisar dinkin duniya ta kafa domin samar da taimako ga kasar Libya tana da kunshe da wakilai wajen metan, kuma tana karkashin jagorancin wani wakili na musamman da babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya nada, kuma muhimmin aikin kungiyar shi ne gudanar da aikin siyasa a kasar Libya.

Kudurin kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya tanada cewa, manyan ayyukan kungiyar taimakawa kasar Libya ta majalisar dinkin duniya sun hada da fannoni da dama, misali, ba da taimako da kuma nuna goyon baya ga kasar Libya da ta maido da kwaciyar hankalin jama'a da tsarin zamantakewar al'umma a kasar, da haka za a sa kaimi ga aikin gudanar da hakokin kasar Libya bisa doka, na biyu, shirya shawarwari ta hanyar siyasa domin tabbatar da sulhuntawa tsakanin kabilu daban daban a kasar, na uku, gudanar da aikin tsara tsarin mulkin kasa da aikin zabe a kasar, na hudu, maido da aikin hidimar jama'a, na biyar, kara kiyaye hakkin dan adam, na shida, nuna goyon baya ga aikin shari'a a lokacin wucin gadi a kasar da kuma daukan wajabtattun matakai domin farfaduwar tattalin arzikin kasar Libya da sauransu.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China