in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori biyu dake gaba da juna a kasar Libya suna ci gaba da musayar wuta
2011-09-19 11:09:40 cri

A ran 18 ga wata, dakarun kwamitin wucin gadi na kasar Libya da sojojin da ke goyon bayan Gaddafi suna ci gaba da yin musayar wuta, a sa'i daya kuma, ba a cimma matsaya ba kan yadda za a kafa sabuwar gwamnati a kasar, shi ya sa, aka jinkirta lokacin kafa sabuwar gwamnatin.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, dakarun kwamitin wucin gadi da sojojin da ke biyayya ga Gaddafi suna ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu a biranen Bani Walid da Sirte. Kakakin sojojin kwamitin wucin gadi ya ce, ko da yake sojojin Gaddafi suna ci gaba da kokarin tunkarar yake-yake, amma ba da dadewa ba ne hukumar  mulki za ta mamaye wadannan wurare.

Kwamitin wucin gadin ya shafe sa'oi 4 yana yin tattaunawa a ran 18 ga wata, amma ba a cimma wata matsaya ba tukuna.

Shugaban gudanarwa na kwamitin wucin gadi na kasar Libya Mahmoud Jibril ya furta a ran 18 ga wata a gun taron manema labaru da aka yi a birnin Banghazi cewa, membobin kwamitin wucin gadi sun cimma matsaya kan galibin ayyukan wasu kwamitocin da ma'aikatu, amma akwai wasu abubuwan da ba a cimma matsaya a kai ba, ana bukatar ci gaba da tattaunawa kan wadannan ayyuka, kafin a kafa sabuwar gwamnatin kasar.

Wani jami'in da ba ya son a bayyana sunansa a kwamitin wucin gadi ya ce, sabuwar gwamnati za ta kunshi kwamitoci da ma'aikatu da yawansu ya kai 22, kana za a canja wasu jami'an tsohuwar gwamnatin kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China