in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar adawa ta kasar Libya za ta tattauna kan batun rufe iyakar kasa tare da kasar Nijer
2011-09-08 15:34:10 cri

Kwamitin wucin gadi na kungiyar adawa ta kasar Libya ya sanar a ran 7 ga wata cewa, zai nemi amincewa daga kasar Nijer dangane da rufe iyakar kasa dake tsakanin su domin hana Moammar Gaddafi da sauran jami'an siyasa shiga kasar Nijer.

Shugaban kwamitin harkokin kasa da kasa na siyasa na kwamitin wucin gadi na kasar Libya Fathi Baja ya gayawa wakilinmu cewa, kwamitin wucin gadi ya yanke shawarar tura tawaga zuwa kasar Nijer domin tattauna batun rufe iyakar kasa tare da kasar Nijer.

Fathi Baja ya ce, kungiyar adawa za ta bukaci dukkan kasashen dake makwabtaka da ita da su hana Gaddafi da kuma muhimman jami'ansa su shiga yankunansu.

A halin yanzu, ana ci gaba da mayar da hankali sosai kan inda Gaddafi yake. Wani jami'in kungiyar adawa ya bayyana a ran 6 ga wata cewa, wani rukunin motoci dauke da wasu jami'ai 11 sun isa kasar Nijer a ran 5 ga wata da dare, kuma wadannan motoci sun yi jigilar dimbin kudi da zinariya mai yawa.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Nijer ya musunta a gun taron manema labaru a ran 6 ga wata cewa, Gaddafi bai shiga cikin kasarsa ba.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China