in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin wucin gadi na kasar Libya na cigaba da yin shawarwari
2011-09-08 13:10:51 cri

Kwamitin wucin gadi na kasar Libya ya sanar da cewa, dole ne magoya bayan Gaddafi su ba da kai kafin ranar 10 ga wata, kawo yanzu, saura kwanaki biyu kawai, amma kwamitin wucin gadi yana cigaba da yin kokari kuma yana fatan zai iya shiga sauran biranen dake karkashin mallakan magoya bayan Gaddafi cikin lumana ta hanyar yin shawarwari. A sa'i daya kuma, har yanzu, ba a san ina Gaddafi yake ba. Saboda haka, kwamitin wucin gadin Libya ya tsai da cewa, zai tura kungiyar wakilai zuwa ga kasar Nijer domin hana Gaddafi da iyalansa tserewa zuwa wannan kasar.

A halin yanzu, kwamitin wucin gadi na duk kasar Libya ya riga ya mamaye yawancin shiyyoyin kasar, amma, garin Gaddafi Sirte da garin Bani Walid dake da nisan kilomita 170 daga kudu maso gabashin Tripoli, babban birnin kasar da garin Sabha dake kudancin kasar suna karkashin magoya bayan Gaddafi. A ranar 7 ga wata, mai kula da shawarwari na kwamitin wucin gadin Libya Abdullah Kenshil ya bayyana cewa, koda yake wakilan da kwamitin ya tura sun janye jiki saboda harin da dakarun magoya bayan Gaddafi suka kai musu a ranar 6 ga wata, amma, kwamitin bai daina yin kokari ba, har yanzu yana fatan zai shiga garin Bani Walid cikin lumana ba tare da zubar da jini ba. Kenshil ya cigaba da cewa, bayan da wasu shugabannin kabilu suka kammala shawarwari da kwamitin wucin gadin Libya, sun gamu da matsaloli tare da dakaru magoya bayan Gaddafi, wasu daga cikinsu sun komo garin Bani Walid, wasu kuma sun je Tripoli. A ranar 7 ga wata, kwamandan aikin soja na kwamitin Abdullah Abu Asara ya bayyana cewa, a halin yanzu, dakarun kwamitin wucin gadin Libya a shirye suke, suna jiran umurni daga hedkwatarsu kuma da zaran ta baso ba bata lokaci take za su kai hari ga garin Bani Walid ta ko wane gefe.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China