in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Niger ta musunta jita-jitar cewa Gaddafi ya shiga kasar
2011-09-07 21:01:32 cri

Shugaban kasar Libya Moammar Gaddafi ya yi batan dabo a yayin da yanayin da ke ciki a kasar ya ci gaba da tsananta, haka kuma a ranar 6 ga wata gwamnatin Niger ta musunta jita-jita cewa Gaddafi ya shiga kasar, amma ta tabbatar da cewa, an amince da babban hafsa mai kula da tsaron Gaddafi da ya shiga kasar, kuma ta ce, ta dauki wannan mataki ne bisa akidar jin kai.

A wannan rana, gwamnatin Burkina Faso ita ma ta bayyana cewa, ba ta samu labarin isawar Gaddafi a kasar ba, kana ba ta samu rokon neman mafaka daga Moammar Gaddafi ba, kuma ba ta zato cewa Gaddafi zai je kasar.

Tuni, kafar yada labaru ta Reuters ta ruwaito cewar majiya daga sojojin kasar Faransa da Niger na cewa, wasu dakaru na Gaddafi dake mallakar manyan motocin yaki kimanin 200 sun shiga yankin arewacin kasar Niger a ran 5 ga wata da dare, ya yiwu Gaddafi zai hadu da wadannan dakaru, sa'an nan za su tafi Burkina Faso. A sa'i daya kuma, a ran 6 ga wata, kakakin kungiyar tsaro ta NATO Roland Lavoie ya jaddada cewa, matakin da NATO ta dauka kan Libya da zummar kiyaye fararen hula, ba ya nufin a kama Gaddafi da mabiyansa. Ya ce, ba zai iya bayani kan sakwanin sirri da NATO ta samu a fili ba. Nato za ta yi amfani da wadannan sakwannin sirri wajen dakile 'yan ta'adda don kiyaye fararen hula.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China