in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NATO ba za ta kama Gaddafi da mabiyansa ba
2011-09-07 15:55:29 cri

Ranar Talata 6 ga wata, kafar yada labaru ta Reuters ta rubuto cewar manazarcin wakilin sojojin kasar Faransa da Niger na cewa, wasu dakaru na Gaddafi dake mallakar manyan motocin yaki kimanin 200 sun shiga Agadez, wani birni dake arewacin kasar Niger a ran 5 ga wata.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, wadannan dakaru sun nufi Niamey babban birnin kasar Niger, ya zuwa yanzu, ba a sani ba ko akwai iyalan Gaddafi da manyan jami'ai dake goyon bayan Gaddafi a ciki ba.

A sa'i daya kuma, a ran 6 ga wata, kakakin kungiyar tsaro ta NATO Roland Lavoie ya jaddada cewa, matakin da NATO ta dauka kan Libya da zummar kiyaye fararen hula, ba yana nufin a kama Gaddafi ba ne da mabiyansa. Ya ce, ba zai iya bayani kan sakwanin sirri da NATO ta samu a fili ba. Nato za ta yi amfani da wadannan sakwannin sirri wajen dakile 'yan ta'addanci da zummar kiyaye fararen hula.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China