in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu sauraro 2 daga kasar Nijeriya sun samu lambar yabo ta musamman a gasar kacici-kacici da CRI ya shirya
2011-09-06 20:49:57 cri

Ranar 6 ga wata, a gidan rediyon CRI da ke birnin Beijing, hedikwatar kasar Sin, an gudanar da bikin ba da lambar yabo ga wadanda suka ci gasar kacici-kacici da rediyon ya shirya don cika shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Nijeriya. Masu sauraro 2 'yan Nijeriya sun samu kyautar musamman da aka bayar.

A madadin rediyon CRI da shugabansa Wang Gengnian, Wang Yunpeng, mataimakin shugban rediyon, ya ba masu sauraron 2 takardun shaida cin gasar. A wajen bikin da aka shirya a wannan rana, Mista Wang ya ce, tun daga shekarar 2005, gidan rediyon CRI yana ta samun cigaba a kokarinsa na kyautata shirin watsa labarai na zamani, wadda ta kunshi sabbin fasahohi daban daban. Saboda haka, a nasa bangare, sashen Hausa na rediyon shi ma ya samu cigaba sosai, wanda ya kara tsawon lokacin watsa labarai a ko wace rana daga sa'o'i 2 zuwa sa'o'i 29 a kasashe daban daban da ke yammacin Afirka, gami da kara wasu hanyoyin watsa labarai da suka hada da tasoshin rediyon FM, da shafin yanar gizo, ban da ta gajeren zango, wanda tun tuni aka fara amfani da shi. Wannan, a cewar Mista Wang, ya bayar da damar fadakar da jama'ar kasashen yammacin Afirka kan kasar Sin.

Malam Nuraddeen Ibrahim Adam daga jihar Kano ta Tarayyar Nijeriya, da Malam Bello Abubakar Gero daga jihar Sokoto ta kasar, sun samu lambar yabo ta musamman, wannan ya ba su damar kawo ziyara nan kasar Sin. Kamar yadda suka bayyana cewa, gasar kacici-kacici da aka shirya ta sa sun fahimci zumuntar dake tsakanin Nijeriya da Sin, kana yadda aka ba su damar ziyarar kasar Sin, ya sa sun kara ilimantuwa sosai a game da tarihi da al'adun al'ummar Sinawa, baya ga samun cikakkiyar damar kulla zumunta da jama'ar kasar Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China