in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kasa cimma matsaya daya a gun shawarwarin tsakanin kungiyar adawa da rundunar soja ta Gaddafi
2011-09-05 21:19:42 cri

Mai kula da harkokin yin shawarwari na kwamitin wucin gadi na kungiyar adawa ta kasar Libya Abdullah Kenshil ya sanar a ran 4 ga wata cewa, an kasa cimma matsaya daya a gun shawarwarin da aka yi tsakanin kungiyar adawa da rundunar soja ta Gaddafi a birnin Bani Walid dake da nisa kilomita dari daya ko fiye zuwa kudu maso gabashin birnin Tripoli.

Abdullah Kenshil ya ce, shugabannin kungiyar adawa za su yanke shawarar ko za a dauki matakin soja nan da nan bayan an kasa cimma nasarar yin shawarwari.

Mustafa Abdel Jalil ya ce, jam'iyyar adawa ta kasar Libya tana fatan sojojin Gaddafi dake biranen Soult da Bani Walid da Jufrah da Sebha za su ajiye makamai kafin ran 10 ga wata, in ba haka ba za a kashe duk wadanda suka ki amsa wannan kiran. Amma jami'an kungiyar adawa dake birnin Bani Walid sun bayyana cewa, tsawon lokacin da suka tsara wa sojojin Gaddafi wajen ba da kai kwanaki 4 kawai.

A game da yanayin kasar Libya, firaministan kasar Algeria ya bayyana a ran 4 ga wata cewa, yana fatan kasar Libya za ta tabbatar da zaman lafiya tun da wuri domin farfado da kyakyawar huldarsu. Wani labari na daban ya ce, wasu sojojin Gaddafi da jami'an hukumar leken asiri sun yi kokarin shiga kasar Algeria a yankin iyakar kasa a tsakanin kasashen Libya da Algeria, amma sun samu adawa daga bangaren Algeria.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China