in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta amince da sakin kaddarorin da aka rike da su na kasar Libya
2011-09-05 20:55:24 cri

A ranar 5 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Jiang Yu ta bayyana cewa, Sin ta amince da sakin kaddarorin da aka rike da su na kasar Libya, kuma kwamitin kula da batun kakabawa Libya takunkumi na kwamitin sulhu na M.D.D ya amince da sakin kaddarorin Libya da wasu kasashen da abin ya shafa suka bayar.

Kwanan baya, kasashen da abin ya shafa suka yi roko ga kwamitin kula da batun sanyawa kasar Libya takunkumi na kwamitin sulhu na M.D.D don neman sakin kaddarorin gwamnatin Libya da aka rike da su a gida, Madam Jiang Yu ta ce, bisa la'akarin moriyar jama'ar kasar Libya, Sin da wasu mambobin M.D.D sun bayyana cewa, kamata ya yi a tabbatar da amfani da kaddarori yadda ya kamata da kafa tsarin sa ido game da wadannanan kudade, kuma bayan da kasashen da suka yi rokon suka kara mika wasu bayanai, an riga an amince da wannan shiri.

Haka kuma, Madam Jiang Yu ta ce, bayan da rikicin Libya ya barke, Sin ta dora muhimmanci sosai kan matsalar jin kai a kasar, kuma ta bayar da agajin jin kai ga jama'ar Libya da kasashen da abin ya shafa. Haka kuma, ta ci gaba da tuntubawar bangarorin biyu na kasar Libya, wajen lallasar su don yin shawarwari.

Kana Jiang Yu ta jaddada cewa, Sin tana taka tsan-tsan wajen fitar da makamai, inda ta tabbatar da cewa ba ta baiwa kasar Libya makamai ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China