Abdullah Kenshil ya ce, shugabannin kungiyar adawa za su yanke shawarar ko za a dauki matakin soja nan da nan bayan an kasa cimma nasarar yin shawarwari.
Mustafa Abdel Jalil ya ce, jam'iyyar adawa ta kasar Libya tana fatan sojojin Gaddafi dake biranen Soult da Bani Walid da Jufrah da Sebha za su ajiye makamai kafin ran 10 ga wata, in ba haka ba za a kashe duk wadanda suka ki amsa wannan kiran. Amma jami'an kungiyar adawa dake birnin Bani Walid sun bayyana cewa, tsawon lokacin da suka tsara wa sojojin Gaddafi wajen ba da kai kwanaki 4 kawai.
A game da yanayin kasar Libya, firaministan kasar Algeria ya bayyana a ran 4 ga wata cewa, yana fatan kasar Libya za ta tabbatar da zaman lafiya tun da wuri domin farfado da kyakyawar huldarsu. Wani labari na daban ya ce, wasu sojojin Gaddafi da jami'an hukumar leken asiri sun yi kokarin shiga kasar Algeria a yankin iyakar kasa a tsakanin kasashen Libya da Algeria, amma sun samu adawa daga bangaren Algeria.(Lami)