in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin goyon bayan Gaddafi sun ki yarda da ba da kai
2011-09-05 13:38:11 cri

A ranar 4 ga wata, rundunar sojojin kwamitin wucin gadi na duk kasar Libya ta yi wa birnin Bani Walid kawanya, tare da shakku cewa, Gaddafi yana boye a nan, hakan ya sa da kyar a mamaye birnin ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. A sa'i daya kuma, kwamitin wucin gadi na duk kasar Libya yana aiwatar da matakai daban daban na sake ginuwar tsarin siyasa da tattalin arziki na kasar.

A halin yanzu, dakarun dake karkashin jagorancin kwamitin sun riga sun mamaye yawancin shiyyoyin kasar Libya, amma masu goyon bayan Gaddafi suna ci gaba da yin yaki da su a wasu garuruwa dake tsakiya da kuma kudancin kasar. A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, bi da bi ne masu goyon bayan Gaddadi da yawansu ya kai fiye da dubu sun shiga birnin Bani Walid dake da nisan kilomita kusan 140 daga Tripoli, babban birnin kasar daga kudancin kasar, cikin dogon lokaci, wannan birnin yana karkashin mamayen kabilar Warfala, kuma 'yan kabilar sun kai miliyan daya a duk fadin kasar Libya, wato yawansu ya kai kashi daya bisa shida na jimillar yawan mutanen kasar. Dakarun adawa da gwamnatin kasar Libya sun dauka cewa, kila Gaddafi yana boye a nan. Kwamitin wucin gadi na duk kasar Libya yana fatan zai mamaye birnin Bani Walid cikin lumana, wakilan rukunoni biyu wato na goyon bayan Gaddafi da na adawa da shi sun riga sun yi shawarwari sau da yawa a cikin kwanakin da suka gabata. A ranar 4 ga wata, kafar watsa labarai da ba ta kasar Libya ba ta ba da labari cewa, wakilan shawarwari na rukunin adawa sun bayyana cewa, shawarwari kan batun birnin Bani Walid ya yi hasara. Yanzu, dakarun adawa sun riga sun yi wa birnin kawanya kuma suna jiran umurnin da za a ba su.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China