in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar adawa ta yi ma Sojojin Gaddafi gargadi na karshe da su bada kai
2011-09-05 10:10:06 cri

Shugaban kwamitin wucin gadi na kasar Libya Mustafa Abdel Jalil ya yi gargadi na karshe ga sojojin Gaddafi, a cewa su bada kai cikin mako daya.

Mustafa Abdel Jalil ya ce, jam'iyyar adawa ta kasar Libya tana fatan sojojin Gaddafi dake biranen Soult da Bani Walid da Jufrah da Sebha za su ajiye makamai kafin ran 10 ga wata, in ba haka ba za a kashe duk wadanda suka ki amsa wannan kiran.

A sa'i daya kuma, jam'iyyar adawa ta kasar Libya ta gaggauta kafa mulkin kasar. Bisa labarin da aka bayar, an ce, jam'iyyar adawa ta riga ta tsara taswirar raya kasa na watanni 20 na wucin gadi, ciki har da kafa kwamitin tsara tsarin mulki a watanni 8 masu zuwa, kuma za a zabi sabon shugaban kasar a cikin watanni 20 masu zuwa.

A game da yanayin kasar Libya, firaministan kasar Algeria ya bayyana a ran 4 ga wata cewa, yana fatan kasar Libya za ta tabbatar da zaman lafiya tun da wuri domin farfado da kyakyawar huldarsu. Wani labari na daban ya ce, wasu sojojin Gaddafi da jami'an hukumar leken asiri suna kokarin shiga kasar Algeria a yankin iyakar kasa a tsakanin kasashen Libya da Algeria, amma sun samu adawa daga bangaren Algeria.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China