in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori biyu na kasar Libya sun ci gaba da yin musayar wuta
2011-08-26 22:03:18 cri

A ran 25 ga wata a birnin Tripoli da sauran yankunan kasar Libya, dakaru masu adawa da gwamnatin kasar da sojojin dake goyon bayan shugaban kasar Moammar Gaddafi sun ci gaba da yin musayar wuta. An kai hari ga dakaru masu adawa a kan hanyar da suke tafiya zuwa garin Gaddafi wato Soult. Kazalika kuma kungiyar adawa tana neman inda Gaddafi ya buya a birnin Tripoli.

A wannan rana a birnin Alkahira dake kasar Masar, shugaban kwamitin wucin gadi na kungiyar adawa ta kasar Libya Mustafa Abdul Jallil ya yi kira ga jama'ar dake zama a yankin dake karkashin jagorancin Gaddafi da su shiga gwagwarmayar juyin juya halin da ake yi. Ya ce, za a baiwa kowane dan kasa hakkinsa, kana kowa zai amfana da dukiyar kasar.

Game da halin da ake ciki a kasar Libya, a ran 25 ga wata, babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa Nabil Elaraby ya bayyana cewa, kungiyarsa ta amince da kwamitin wucin gadi na kungiyar adawa ta kasar Libya a matsayin halattacciyar wakiliyar jama'ar kasar.

Hakazalika kuma, a ran 25 ga wata a birnin Istanbul dake kasar Turkiya, rukunin tattauna batun kasar Libya da ya kunshi kasashe 28 da kungiyoyin duniya 7 ya gudanar da wani taro, inda aka jaddada da cewa, kwamitin wucin gadi na kasar Libya shi ne halattacciyar wakiliyar kasar da jama'arta, kana masu halartar taron sun tattauna kan yanayin kasar Libya bayan yakin da kuma batun bada taimako ga kasar a fannin tattalin arziki.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China